logo

HAUSA

Sin da kasashen Afrika masu magana da Faransanci sun shirya taro ta kafar bidiyo game da demokuradiyya

2022-04-27 10:51:35 CMG Hausa

A jiya Talata, kasar Sin ta gudanar da taron karawa juna sani ta kafar bidiyo da kasashen Afrika 22 masu magana da yaren Faransanci mai taken “Bincike da amfani da demokuradiyya a majalisun dokokin kasashen Sin da Afrika".

Ding Zhongli, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) ya halarci bikin kaddamar da taron na kwanaki biyu inda ya ba da wani jawabi.

Mr. Ding ya bayyana cewa, majalisar NPC a shirye take ta yi aiki tare da majalisun dokokin kasashen Afrika domin bayar da gudunmawa wajen aiwatar da hakikanin demokuradiyya da kuma ingantaccen tsarin demokuradiyya mafi dacewa da kasashensu, don ci gaba da inganta zaman rayuwar al’ummun dukkan kasashen, da bunkasa tsarin demokuradiyyar da zai kyautata huldar kasa da kasa. (Ahmad)