logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin inganta kayayyakin more rayuwa a kasar

2022-04-27 11:28:18 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taro na 11 na kwamitin kula da aikin kudi da raya tattalin arziki na kasar a jiya Talata, inda manyan jami’ai mahalarta taron suka yi bitar yadda za a ci gaba da inganta kayayyakin more rayuwa a kasar, da yanayin da ake ciki wajen aiwatar da tsare-tsaren da kwamitin ya gabatar a baya.

A wajen taron, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ingancin kayayyakin more rayuwa, tushe ne ga ci gaban tattalin arziki da na zamantakewar al’umma, saboda haka ya kamata a daidaita aikin raya tattalin arziki da tsaro, da kyautata tsarin gina kayayyakin more rayuwa, don ya zama mai kunshe da fasahohin zamani, ta yadda za a aza harsashi mai karfi ga aikin gina wata kasar zamani mai bin tsarin siyasa na gurguzu. (Bello Wang)