logo

HAUSA

Krishna Srinivasan: Sin ta zama jigon wanzuwar tsarin samar da hajoji da ci gaban amfani da makamashi ba tare da gurbata muhalli ba

2022-04-27 14:46:24 CMG Hausa

A baya bayan nan, sakamakon bincike da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar, ya nuna cewa, rikicin Rasha da Ukraine, da kuma bazuwar cutar COVID-19, baya ga mummunan tasirin su ga habakar tattalin arzikin duniya, sun kuma yi matukar tasiri ga tsarin samar da hajoji na duniya, da ma tsarin amfani da makamashi maras gurbata muhalli.

Da yammacin ranar Litinin 25 ga watan nan, mataimakin daraktan sashen Asiya da Pacifik a bankin na IMF Krishna Srinivasan, ya amsa tambayar da wakilin kafar talabijin ta CCTV ya gabatar masa, inda ya ce Sin ta zama jigon wanzuwar tsarin samar da hajoji, da ci gaban amfani da makamashi ba tare da gurbata muhalli ba.  (Saminu)