logo

HAUSA

Dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD sun tsaurara ayyukan tsaro a yankin Menaka na Mali

2022-04-27 11:00:12 CMG Hausa

Jami’an wanzar da zaman lafiya na MDD suna ci gaba da tsaurara ayyukan tabbatar da tsaro da ba da kariya a shiyyar Menaka na kasar Mali, yayin da ake fuskantar karuwar tashin hankali. Mai magana da yawun MDD ya bayyana hakan a ranar Talata.

Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren MDD ya bayyana cewa, tawagar dakarun sojoji da jami’an ’yan sanda na MDDr dake Mali, wadanda aka fi sani da MINUSMA, gami da dakarun tsaron kasar Mali, sun gudanar da ayyukan farmaki a dare da rana a yankin Menaka. Tabarbarewar yanayin tsaro da aka samu a makonnin baya bayan nan ne ya tilastawa dakarun tsaron daukar matakan wanzar da zaman lafiyar.

Tawagogin suna kuma ci gaba da ayyukan bayar da tallafin jinkan bil adama ga mutanen dake cikin yanayin matukar bukata, sannan jami’an tsaron suna cigaba da bada himma wajen dakile barkewar rikicin kabilanci a tsakanin al’ummun yankunan kasar. (Ahmad)