logo

HAUSA

Manufar Sin daya tak shi ne tushen zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan

2022-04-27 21:44:55 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, manufar kasar Sin daya tilo a duniya ita ce ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan.

An ruwaito cewa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya bayyana a kwanan baya a wani zaman majalisar dokokin Amurkar cewa, gwamnati Amurka ta kuduri aniyar tabbatar da cewa, yankin Taiwan yana da dukkan hanyoyin da suka dace, don kare kansa daga duk wani yunkuri na takalarsa.

Wang Wenbin ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa cewa, muna adawa da ma watsi da kalaman na Antony Blinken.

Wang ya kara da cewa, bai kamata bangaren Amurka ya raina hakikanin kuduri, da karfin da jama'ar kasar Sin biliyan 1.4 suke da shi, wajen kare ikon mallakar kasa da cikakkun yankinsu ba. Wannan kudiri na Amurka, babu abin da zai haifar illa tura yankin Taiwan ramin da ba zai iya fita ba da kuma mummunan sakamako da hakan zai haifar ga ita kanta Amurka .