logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin jami’ar Karachi

2022-04-27 11:19:41 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin bam da ya auku a jami’ar Karachi ta kasar Pakistan, wanda ya haddasa kisan wasu malamai Sinawa su 3, tare da jikkata wani malami Basine daya, da karin wasu ‘yan kasar Pakistan da dama.

Mataimakin kakakin magatakardar MDD Farhan Haq, ya ce baya ga Mr. Guterres, shi ma babban jami’in MDD, kuma jagoran ofishin tsare tsaren majalissar a Pakistan Julien Harneis, sun yi matukar Allah wadai da harin na jiya Talata.

A nasa bangare, kakakin ma’aikatar wajen kasar Sin, ya ce abun fashewar ya tarwatsa mota kirar Bas dake jigilar jama’a, mallakin cibiyar koyar da al’adun Sinawa ta Confucius dake jami’ar ta Karachi.

Ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ofishin jakadancin kasar dake Pakistan, za su ci gaba da aiki tukuru tare da sassan Pakistan da lamarin ya shafa, domin baiwa wadanda suka jikkata kulawa, da kuma tabbatar da an hukunta kungiyoyin ta’addanci dake da hannu cikin aikata wannan ta’asa. Jami’in ya kara da cewa, ko alama jinin Sinawa ba zai zuba a banza ba, kuma wadanda suka aikata wannan laifi za su girbi mummunan sakamako.  

Bayan aukuwar lamarin, firaministan Pakistan Shabazz Sharif, ya gabatar da wasikar ta’aziyya, kana ya ziyarci ofishin jakadancin kasar Sin domin bayyana ta’aziyyar rasuwar Sinawa da harin ya rutsa da su.

Firaminista Sharif ya yi Allah wadai da duk wani nau’in harin ta’addanci. Yana mai cewa, mugun shirin makiya ba zai taba gurgunta kyakkyawar alaka da abota dake tsakanin Sin da Pakistan, kuma ba zai dakile hadin gwiwar sassan 2 ba. (Saminu)