logo

HAUSA

Xi ya taya murnar taron musayar kirkire-kirkire na farko na kwararrun ma’aikata masu sana’o’i daban daban

2022-04-27 21:00:19 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar kirkire-kirkire na farko na kwararrun ma’aikata masu sana’o’i daban daban na kasar da aka bude Larabar nan a birnin Beijing.

Xi, ya yi kira a gare su da su ba da gudummawar hikima da karfi, don samun ci gaba mai inganci da aiwatar da dabarun gina kasa, ta yadda kasarsu za ta zama jagora a fannin kere-kere.

Shugaba Xi ya kuma mika sakon gaisuwa ga kwararrun ma'aikata, da ma'aikata dake zama abin koyi da daukacin ma’aikata, gabanin ranar ma'aikata ta kasa da kasa.