logo

HAUSA

Vladimir Putin da Antonio Guterres sun tattauna batun rikicin Ukraine

2022-04-27 10:23:37 CMG Hausa

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, a fadar Kremlin ya gana da babban sakataren MDD Antonio Guterres wanda ya kai ziyarar aikinsa a Rasha a ranar Talata, inda suka tattauna game da yanayin da ake ciki a Ukraine.

Putin ya ce, “duk da yanayin matakan soja da ake ci gaba da fuskanta, muna fatan za mu iya cimma matsaya ta hanyar diflomasiyya. Muna kokarin daidaitawa, kuma ba za mu juya musu baya ba.”

Gabanin ziyararsa a Moscow, Guterres ya gana da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a Ankara, babban birnin kasar a ranar Litinin. Jami’in MDDr zai zarce zuwa Ukraine bayan kammala tattaunawa da Putin. (Ahmad)