logo

HAUSA

An kai harin ta'addanci kan motar bas ta kwalejin Confucius a Jami'ar Karachi

2022-04-26 21:57:40 CMG Hausa

Da misalin karfe 2:20 na yammacin ranar yau Talata agogon wurin, aka kai hari kan motar bas ta kwalejin Confucius na Jami'ar Karachi a harabar jami'ar. Ya zuwa yanzu lamarin ya haddasa rasuwar malamai 3 ‘yan kasar Sin, sannan wani ya jikkata.

Ofishin jakadanci da karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Pakistan sun yi Allah wadai da wannan aikin ta'addanci, tare da jajantawa wadanda suka rasa rayukansu, kuma za su yi duk mai yiwuwa wajen daidaita lamarin tare da bangaren Pakistan. (Mai fassara: Bilkisu Xin)