logo

HAUSA

Masanin Najeriya ya yi tsokaci kan matsayar Sin game da rikicin Ukraine

2022-04-26 11:48:32 CMG HAUSA

 

Ranar 21 ga watan Afrilun shekarar 2022, Olalekan Babatunde, wani manazarci daga cibiyar nazarin zaman lafiya da warware rikici ta Najeriya, ya wallafa wani sharhi mai taken “Bayani dalla-dalla game da matsayar kasar Sin dangane da rikicin Ukraine” inda aka wallafa a wasu daga cikin manyan jaridun Najeriya na "This Day" da "The National". Sharhin ya yi tsokaci cewa, tarihi na baya bayan nan ya tabbatar da cewa, kasar Sin ba ta kaunar yaki da ma dukkan wani nau’in tashin hankali. Matsayin kasar Sin game da rikicin kasar Ukraine, ya nuna aniyar kasar na son zaman lumana.

Sharhin ya bayyana cewa, matsayar kasar Sin shi ne, ba ta nuna goyon baya ga kasar Rasha ko kuma nuna adawa ga Ukraine ba, amma duk da hakan tana shan suka daga kasar Amurka, da kasashen yamma da kuma kungiyar NATO. Yunkurin fadada ikon kungiyar NATO a gabashin Turai shi ne musabbabin da ya haifar da barkewar rikicin. Kasar Sin ta nuna halin dattaku a matsayinta na wata babbar kasa, kuma ya kamata sauran kasashe masu kima su bi sahun kasar Sin wajen nuna goyon bayan amfani da hanyoyi na diflomasiyya don warware rikicin. (Ahmad Fagam)