logo

HAUSA

Sin za ta nace ga amfani da sararin samaniya lami lafiya don amfanin dukkanin Bil Adama

2022-04-26 10:26:28 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jadadda a gun taron manema labarai da aka yi a jiya Litinin, cewar Sin tana nacewa ga matsayin amfani da sararin samaniya lami lafiya don kawowa dukkanin bil adama alheri.

An ba da labarin cewa, hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin ya bayyana cewa, Sin za ta kafa tsarin kare doron duniyarmu daga barzanar da mai yiyuwa ne wasu kananan taurarin wadanda suke kusa da ita za su kawo mata. Yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da ko kasar Sin za ta yi hadin gwiwar sauran kasashen duniya a wannan fanni, Mr. Wang Wenbin ya ce:“Sin na tsaiwa tsayin daka, kan matsayin amfani da sararin samaniya lami lafiya, don kawowa dukkanin Bil Adama alheri, kuma Sin ta kafa wannan tsari ne don kare duniyarmu, idan akwai hadarin cin karon ta da wasu kananan taurarin dake kusa da ita. Sin za ta ci gaba da mu’ammala, da hadin kai da kasa da kasa, karkashin tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban na MDD, ciki har da kwamitin amfani da sararin samaniya lami lafiya na MDD da sauransu, don taka rawarta wajen kiyaye lafiyar doron duniyarmu.”  (Amina Xu)