logo

HAUSA

Duniya na bukatar Turai mai cin gashin kai

2022-04-26 10:13:32 CMG HAUSA

 

A ranar Lahadin da ta gabata, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya sake lashe zaben shugabancin kasarsa a karo na 2. A matsayin Faransa na kasa mai muhimmanci a tarayyar Turai, ta kasance ginshikin dunkulewa, da nacewa manufar cin gashin kan nahiyar. Game da sabon yanayi na barkewar yake-yake a Turai, sake zaben shugaba Macron ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki.

Batun ’yancin kai, ginshiki ne cikin manufofin harkokin wajen kasar Faransa. Zangon mulkin Macron na farko ya maida hankali ga kyautata matsayin ’yancin Faransa da Turai tsakanin kasarsa ko nahiyar Turai da sauran kasashen duniya, musamman batun "rage dogaro ga wasu karkashin wasu kawance".

A watan Satumbar shekarar bara, lokacin da Faransa ta fuskanci murzunawa daga Amurka, da Birtaniya da Australia, ta kuma yi asarar kwangilar dala biliyan 65, ta cinikayyar jiragen yakin karkashin teku da Australia ta bukata, shugaba Macron ya fito fili ya bayyana Amurka a matsayin kasa, wadda har kullum ke matukar sanya moriyarta gaban komai, Ya ce "Ya zama wajibi Turai ta yi watsi da rashin kwarewa. Dole ne mu nuna muna iya kare kanmu a duk lokacin da muka fuskanci matsi daga masu karfin fada a ji".

A yayin takarar neman zabensa, Macron ya ce zai ci gaba da aiwatar da manufofin zangon gwamnatinsa ta farko, zai samar da Faransa mai karin ’yanci. Wannan ne ma ya haifar masa da samun goyon baya, ko da yake hakan zai zamo masa kalubale bayan lashe zaben da ya yi.    (Saminu)