logo

HAUSA

Artemisinin wata nasara ce da aka samu wajen zama tsintsiya madaurinki guda a tsakanin Sin da kasashe masu tasowa

2022-04-26 20:32:08 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba gudanarwa a yau Talata cewa, kwayar maganin artemisinin, wata nasara ce da kasar Sin ta samu wajen zama tsintsiya madaurinki guda da dimbin kasashe masu tasowa, ta kuma haifar da alfanu ga duniya ta hanyar ci gabanta.

Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta taimakawa duniya wajen yin amfani da artemisinin, wanda ya ceto rayukan miliyoyin jama'a a duniya, musamman a kasashe masu tasowa, ana iya cewa, ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen yaki da cutar malariya a duniya, da kiyaye kiwon lafiyar dan Adam. Alkaluman kididdigar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar sun nuna cewa, kimanin mutane miliyan 240 a yankin kudu da hamadar Sahara kadai sun amfana da maganin artemisinin. (Mai fassara: Bilkisu)