logo

HAUSA

Kasar Sin ta bude bangaren dawowa na Shenzhou-13

2022-04-26 19:36:36 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana Talatar nan cewa, an bude bangaren dawowa na kumbun Shenzhou-13, wanda ya dawo da 'yan sama jannatin nan guda uku zuwa doron duniya a ranar 16 ga watan Afrilu.

Kayayyakin da kumbon ya dauko, sun hada da irin amfanin gona, da ma’adanin bayanai mai girman 8K da aka adana hotuna da bidiyon da ‘yan sama jannati suka dauka a sararin samaniya, da tambarin tunawa, da kuma zanen da matasan Hong Kong suka yi, kuma duk an fitar da su daga cikin bangaren dawowa na kumbon.

A ranar 16 ga watan Oktoban shekarar 2021 ne, aka harba kumbon Shenzhou-13 daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan da ke arewa maso yammacin kasar Sin. A lokacin da kumbon ke cikin falaki, an yi nasarar gudanar da gwaje-gwaje a fannin kimiyya da fasahar sararin samaniya.