logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi rangadin aiki a jami'ar Renmin ta kasar Sin

2022-04-25 16:04:21 CMG Hausa

Kafin ranar 4 ga watan Mayu, wato ranar matasa, Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar ya yi rangadin aiki a jami'ar Renmin ta kasar Sin da safiyar ranar Litinin 25 ga watan nan, inda ya shiga cikin ajujuwan siyasa da ake amfani da na’urori masu kwakwalwa wajen gudanar da su, da dakin adana kayayyakin tarihi, da dakunan karatu. Ya kuma kara fahimtar yadda jami’ar take kokarin yin gyare-gyaren dabarun koyar da darussan siyasa, da tarihin jami’ar, da nasarorin da aka samu daga wajen aikin koyarwa, da karfafa kare da kuma amfani da tsofaffin adabi da littattafan tarihi, har ma yadda jami’ar take mayar da sakamakon bincike ya zama abubuwa a zahiri da dai sauransu. Sannan ya jagoranci taron kara wa juna sani da wakilan malamai da dalibai suka halarta. (Safiya Ma)