logo

HAUSA

Ranar Malaria Ta Duniya: Ga yadda kwararrun Sin ke taimakawa Sao Tome da Principe yaki da malaria

2022-04-25 10:58:12 CMG Hausa

Ranar 25 ga watan Afrilu rana ce ta yaki da cutar Malaria ta kasa da kasa. Guo Wenfeng, wani kwararren likita ne daga tawagar kwararrun masu bada agajin kiwon lafiya ta kasar Sin dake yaki da zazzabin cizon sauro wato malariya a tsibirin Sao Tome da Principe, ya bayyana yadda suke gudanar da aikinsu na yaki da cutar malariya a wannan yanki.

Yaki da cutar malariya ya kasance daya daga cikin muhimman bangarorin kiwon lafiya na hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Sao Tome da Principe.

Idan aka yi la’akari da irin nasarorin da aka cimma a halin yanzu, kuma idan aka kwatanta da hakikanin yanayin da ake ciki a tsibirin São Tomé da Príncipe, kasar Sin ta taimakawa São Tomé da Príncipe wajen tsara sabbin dabarun yaki da malariya wadanda suka fi mayar da hankali wajen dora dukkan mutane kan amfani da magunguna, gami da wasu dabarun dakile hayayyafar sauro, matakan sun haifar da muhimman sakamako a kauyuka da dama da cutar malariya ta yi kamari. Domin kara fadada sakamakon da aka samu na yaki da cutar malariyar, bayan hadin gwiwa da ma’aikatar kiwon lafiyar São Tomé da Príncipe, tagawar kasar Sin dake yaki da cutar malariyar, za ta gudanar da aikin gangamin rabon magunguna na kasa baki daya a wasu kauyuka 10 inda matsalar cutar malariyar ta fi tsanani, a shiyyar Agua Grande tsakanin watan Maris zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Guo Wenfeng ya yi amanna cewa, ta hanyar hadin gwiwar kut-da-kut tsakanin tawagogin yaki da cutar malariyar na Sin da Sao Tome da Principe, shirin zai yi matukar tasiri wajen rage girman matsalar cutar malaria, kuma zai inganta rayuwar mazauna wurin, kana zai taimakawa tsibirin Sao Tome da Principe wajen cimma nasarar muradun kawar da cutar malariya baki daya nan da shekarar 2025. (Ahmad)