logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon wasika don taya murnar cika shekaru 50 da samar da kwayar maganin Artemisinin

2022-04-25 14:58:57 CMG Hausa

A yau 25 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon wasika don taya murnar cika shekaru 50 da samar da kwayar magani ta Artemisinin da dandalin kasa da kasa na tallafawa gina lafiyar al’umma.

Xi Jinping ya bayyana cewa, kwayar maganin artemisinin shi ne maganin yaki da cutar malariya mafi inganci da aka gano kuma aka cimma nasarar samar da shi a kasar Sin. Maganin ya taimakawa kasar Sin wajen kawar da cutar malariya baki daya daga kasar a shekaru 50 da suka gabata. A don haka, artemisinin ya samu shahara da karbuwa a duk duniya, ya ceto miliyoyin rayukan jama’a a sassan duniya, musamman a kasashe masu tasowa.

Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da al’ummun kasa da kasa, wajen karfafa hadin gwiwa a fannin kula da lafiyar al’umma, da hadin gwiwa don yin aiki tare wajen tinkarar manyan kalubalolin dake wa duniya barazana, domin bayar da gagarumar gudunmawa wajen kiyaye lafiyar al’ummar dukkan kasashen duniya. (Ahmad)