logo

HAUSA

Kwayar maganin Artemisinin ta zama muhimmin taimako na kasar Sin wajen yakar malariya

2022-04-25 11:41:24 CMG Hausa

A yau 25 ga wata, rana ce ta yaki da cutar malariya ta kasa da kasa. Hukumar bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin, da hukumar lafiya ta kasa, da hukumar kula da magungunan gargajiyar kasar Sin, sun yi hadin gwiwa don shirya bikin cika shekaru 50 da samar da kwayar maganin malaria ta Artemisinin, da taimakawa wajen gina dandalin kula da lafiyar al’umma na kasa da kasa, jami’an diflomasiyyar kasashe da dama dake kasar Sin, da shugabannin hukumomin kasa da kasa dake kasar Sin sun halarci taron.

Deng Boqing, mataimakin shugaban hukumar bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin, ya bayyana a wata tattaunawa cewa, tun daga shekarar 2012, kasar Sin ta taimakawa kasashe masu tasowa wajen yakar cutar malaria ta hanyar samar musu da kwayar maganin artemisinin, da horas da jami’an lafiya, da kuma tura tawagogin kwararrun kiwon lafiya, da gina cibiyoyin yaki da cutar malariya. Kawo yanzu, sama da ayyuka daban-daban na tallafawa yaki da cutar malaria guda 300 aka aiwatar,  sannan an tallafa wajen gina cibiyoyin yaki da cutar malariyar a kasashe 30, da tura tawagogin jami’an tallafin kiwon lafiya 28,000 zuwa kasashen duniya da shiyyoyi 72, sannan an horas da dubban jami’an lafiya game da yaki da cutar malariya a kasashe masu tasowa. Da samar da kwararrun masana yaki da malaria. A yanzu, kwayar maganin Artemisinin ta zamto wani muhimmmin ginshikin kasuwanci da kuma taimako a yaki da cutar malariya, matakin da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga shirin yaki da malariya a duniya. (Ahmad)