logo

HAUSA

Macron ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Faransa

2022-04-25 10:48:43 CMG Hausa

Shugaban kasar Faransa mai ci Emmanuel Macron, ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na shekarar 2022 da kashi 58.6 bisa 100 na kuri’un da aka kada, kamar yadda sakamakon farko na zaben da aka fitar a ranar Lahadi wanda gidan talabijin din kasar na BFMTV ya gabatar.

Abokiyar fafatawar Macron, wacce ta tsaya takarar karkashin jam’iyya mai tsattsauran ra’ayi Marine Le Pen, ta samu kashi 41.4 bisa 100 na kuri’un, kamar yadda alkaluman baya bayan nan na zaben suka nuna.

Biyo bayan nasarar da ya samu, Macron ya shiga lambun shakatawa na Champs-de-Mars, yana rike da hannun matarsa, inda ya samu rakiyar gangamin matasa a kewaye dashi, sannan ana rera take na yankin Turai na "Ode to Joy" na Beethoven.

Macron ya ce, babban burinsa nan da shekaru biyar shi ne ya tabbatar da kasar Faransa ta samu karin ’yanci, da kara karfin Turai, da ci gaba da zuba jari don mayar da kasar Faransa a matsayin wata babbar kasa ta fuskar muhallin halittu. (Ahmad)