logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya Macron murnar sake lashe zaben shugaban kasa

2022-04-25 15:35:45 CMG Hausa

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kira takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ta wayar tarho, inda ya taya shi murnar sake lashe zaben shugaban kasa a karo na 2.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da Faransa manyan kasashe ne masu al’adar cin gashin kai. Ya ce a yanzu, yanayin kasa da kasa na sauyawa cikin salo mai sarkakiya, kuma managartan dabarun ci gaban kasar Sin da Faransa na kara fitowa fili.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, har kullum yana maida hankali ga yadda alakar Sin da Faransa ke bunkasa cikin tsawon lokaci, yana kuma fatan ci gaba da aiki tare da shugaba Macron, wajen ingiza alakar kasarsa da Faransa zuwa sabon matsayi. (Saminu)