logo

HAUSA

Yadda kasar Sin ta baiwa fannin lafiyar duniya tagomashi

2022-04-25 16:05:04 CMG Hausa

Masu hikimar magana na cewa, “yabon gwani ya zama dole.” Yayin da ranar 25 ga watan Afrilu ta kasance a matsayin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya ta kasa da kasa, ko shakka babu, duniya ba za ta taba mantawa da dunbun alheran da kasar Sin ta samar ga fannonin daban-daban ba, musamman fannin kiwon lafiyar bil adama. Albarkacin wannan rana ta bikin yaki da cutar maleriya ta shekarar 2022, bari mu yi tsokaci kan wata muhimmiyar gudummawa da kasar Sin ta baiwa duniya wajen yaki da cutar maleriya.

Kwayar maganin Artemisinin, wani magani ne da ya shahara a duniyar yaki da cutar maleriya, maganin, wanda kasar Sin ne ta kirkiro bisa fasahar amfanin tsirrai. A bana, ake murnar cika shekaru 50 da kasar Sin ta samar da tare da fara amfani da maganin Artemisinin. A sakon da ya aike, shugaba Xi Jinping ya taya murna ga dandalin kasa da kasa bisa murnar cika shekaru 50 da samar da kwayar maganin Artemisinin don gina lafiyar jikin al’umma. Hakika, kwayar maganin Artemisinin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar maleriya ga duniya. A cikin kalaman shugaban, ya bayyana cewa, kwayar maganin Artemisinin shi ne maganin yaki da cutar maleriya mafi inganci da aka gano kuma aka cimma nasarar samar da shi a kasar Sin. Maganin ya taimakawa kasar Sin wajen kawar da cutar maleriya baki dayanta daga kasar a shekaru 50 da suka gabata. A don haka, artemisinin ya samu shahara da karbuwa a duk duniya. Wani abin farin ciki shi ne, baya ga tasirin da maganin ya haifar wajen kakkabe cutar daga kasar Sin, sannan ya taimaka wajen ceto miliyoyin rayukan jama’a a sassan duniya, musamman a kasashe masu tasowa. A cewar Deng Boqing, mataimakin shugaban hukumar bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin, daga shekarar 2012, kasar Sin ta taimakawa kasashe masu tasowa wajen yakar cutar maleriya ta hanyar samar musu da kwayar maganin Artemisinin, da horas da jami’an lafiyarsu, da kuma tura tawagogin kwararrun masana kiwon lafiya, da gina cibiyoyin yaki da cutar maleriya. Kawo yanzu, an aiwatar da ayyuka daban-daban na tallafawa yaki da cutar maleriya a kalla 300, sannan an tallafa wajen gina cibiyoyin yaki da cutar maleriyar a kasashe 30, da tura tawagogin jami’an tallafin kiwon lafiya 28,000 zuwa kasashen duniya da shiyyoyi 72, sannan an horas da dubban jami’an lafiya game da yaki da cutar maleriya a kasashe masu tasowa. Da samar da kwararrun masana yaki da malaria.

A yanzu, kwayar maganin Artemisinin ta zamto wani muhimmmin ginshikin kasuwanci da kuma taimako a yaki da cutar malariya, matakin da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga shirin yaki da malariya a duniya. Koda yake za mu iya cewa, wannan batu bai zo da mamaki ba, kasancewa a ko da yaushe, mahukuntan kasar Sin sun sha nanata aniyar cewa kasar a shirye take ta yi aiki tare da al’ummun kasa da kasa, wajen karfafa hadin gwiwa a fannin kula da lafiyar al’umma, da hadin gwiwa don tinkarar manyan kalubalolin dake yiwa duniya barazana da nufin bayar da gagarumar gudunmawar kiyaye lafiyar al’ummar kasashen duniya don a gudu tare a tsira tare. (Ahmad Fagam)