logo

HAUSA

Kasar Sin za ta nace kan manufar bai daya ta yaki da COVID duk da yadda hakan ka iya shafar tattalin arziki

2022-04-25 21:39:31 CMG Hausa

A yau ne, kasar Sin ta rubanya manufarta ta dakile cutar COVID-19 da zarar an gano ta, inda ta tabo batun shawarar masana kimiyya da amincewa da yadda matakin ka iya shafar tattalin arziki, biyo bayan dakatar da aikin samar da wasu kayayyaki.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai cewa, irin wannan manufa ya dace da halin da kasar Sin take ciki da kuma ka'idojin hukumar lafiya ta duniya.Yana mai cewa,wadannan matakan, sun tabbatar da tsaro da lafiyar Sinawa da ma 'yan kasashen waje mazauna kasar Sin yadda ya kamata.

Alkaluma sun nuna cewa, adadin wadanda suka mutu sanadiyar annobar COVID-19 a kasar Sin a shekarar 2021 0.4 ne cikin mutum 100,000 da suka kamu da cutar, adadin da ya kai kashi 1 bisa 606 na kasar Amurka. Kuma kasar Sin na daya daga cikin kasashen da ba a samu mutuwa sosai sakamakon COVID-19 a duniya ba

Wang ya ce, galibin Sinawa sun fahimta kuma suna goyon bayan matakan rigakafi da kasar ke aiwatarwa, suna kuma cike da kwarin gwiwa kan yaki da cutar.