logo

HAUSA

An kafa cibiyar nazarin kididdigar da taurarin dan Adam ke samarwa ta hadin gwiwar kasa da kasa a lardin Hainan na Sin

2022-04-25 11:11:10 CMG Hausa

Da safiyar jiya Lahadi ne aka gudanar da bikin murnar “Ranar Sararin Samaniya Ta Kasar Sin” ta shekarar 2022 ta yanar gizo, wanda ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta Sin, da hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta Sin, da kuma gwamnatin lardin Hainan na Sin suka karbi bakuncin gudanar da shi.

Mataimakin babban direktan hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta Sin Wu Yanhua ya yi jawabi ta yanar gizo, inda ya ce, an kafa cibiyar nazarin kididdigar da taurarin dan Adam ke samarwa da hadin gwiwar sassan kasa da kasa ta hukumar, da kuma cibiyar kula da kididdigar da tauraron dan Adam da ake sarrafawa daga nesa ta kungiyar BRICS ta kasar Sin, inda karkashin hakan ake fatan sa kaimi ga yin amfani da kididdigar a tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata. Wu ya ce,“Hukumar kula da sararin samaniya ta Sin, ta tsai da kudurin kafa cibiyar nazarin kididdigar da tauraron dan Adam ke samarwa ta hadin gwiwar kasa da kasa a lardin Hainan, don samar da hidimar nazarin kididdigar ga duniya baki daya. Kana cibiyar za ta zama hukumar nuna goyon baya ga cibiyar kula da kididdigar da tauraron dan Adam da ake sarrafawa daga nesa na kungiyar BRICS ta kasar Sin, da sa kaimi ga cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa na MDD nan da shekarar 2030, don samar da gudummawar Sin ga raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama.” (Zainab)