logo

HAUSA

Wang Yi: Kasar Sin ta bayar da muhimmiyar gudunmawa ga hadin gwiwar yaki da annoba

2022-04-25 16:11:47 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron dandalin kasa da kasa na cika shekaru 50 da samar da kwayar maganin Artemisinin don kare lafiyar al’umma.

Wang Yi ya bayyana cewa, yayin da ake fama da cutar COVID-19 annobar mafi muni a wannan karni, kasar Sin ta dauki matakan ci gaba tare da kaddamar da ayyukan gaggawa na jinkan bil adama mafi girma. Kawo yanzu, kasar Sin ta samar da magungunan yaki da annobar na biliyoyin kudi, inda aka rarraba a kasashen duniya 153, da kungiyoyin kasa da kasa 15, ta samar da kwalaben riga-kafin cutar biliyan 2.2 ga kasashen duniya 120 da kungiyoyin kasa da kasa, kana ta tura tawagogin kwararrun jami’an kiwon lafiya 37 ga kasashe 34. Bugu da kari, kasashe fiye da 180 da kungiyoyin kasa da kasa sun yi musayar kwarewa da kasar Sin a fannin kandagarki da yaki da annobar. (Ahmad)