logo

HAUSA

Wasu mahara sun hallaka sojoji 6 a tsakiyar kasar Mali

2022-04-25 11:04:37 CMG Hausa

Wasu ’yan bindiga sun kaddamar da hare hare a Niono da Bapho, da kuma sansanin sojoji na Sevare dake tsakiyar kasar Mali da sanyin safiyar jiya Lahadi, lamarin da ya haddasa rasuwar sojojin kasar su 6, da maharan 11, an kuma jikkata karin wasu mutane sama da 10.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, darektan watsa labarai da hulda da jama’a na rundunar sojin kasar ta Mali, ko “Dirpa” a takaice, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, maharan sun kaddamar da farmakin ne a wurare 3 kusan a lokaci guda, inda a sansanin Sevare suka yi amfani da wata mota makare da ababen fashewa, don kutsawa cikin sansanin, sai dai sojoji sun mai da martani da barin wuta, lamarin da ya dakile yunkurin nasu. (Saminu)