logo

HAUSA

Ma’aikatan kwadago a Xinjiang na da ‘yancin gudanar da ayyukansu

2022-04-24 17:20:53 CMG Hausa

Kakakin gwamnatin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur dake arewa maso yammacin kasar Sin, Xu Guixiang ya sanar cewa, ma’aikatan kwadago ‘yan kabilu daban daban na jihar suna da ‘yancin zabar sana’o’in da suke son yi kuma bisa radin kansu.

Xu Guixiang, ya bayyana a taron manema labarai a Beijing cewa, yankin Xinjiang yana bin dokokin kungiyar kwadago ta kasa da kasa, kuma ana aiwatar da dokokin kasa yadda ya kamata, sannan ana tabbatar da cewa ma’aikata daga dukkan kabilun yankin suna gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci.

Xu ya ce, sakamakon matsanancin muhallin halittu da kuma koma bayan cigaban tattalin arziki, a shekarun baya, an fuskanci matsalar ‘yan kwadago fiye da yadda ake bukata a yankunan karkarar kudancin jihar. Don haka, mazauna karkara a kudancin Xinjiang, sun gamu da walwalu wajen neman guraben ayyukan yi.

Ya ce, a shekaru da dama, gwamnatoci na dukkan matakai a Xinjiang, sun yi ta kokarin daukar matakan taimakawa matalauta don fitar dasu daga kangin talauci, ta hanyar taimaka musu wajen samun ayyukan yi a sauran wurare.

Xu ya ce, wannan ba aikin kwadago na tilas ba ne, ya kara da cewa, mutane suna da ‘yancin yanke shawarar ko za su iya barin gidajensu, da inda za su je, da kuma irin ayyukan da suke son yi.

Xu ya kara da cewa, yayin da suka fara samun kudaden shiga daga sabbin ayyukan nasu, mutane da dama sun sayi gidaje, da motoci, kuma sun samu jarin da zasu kafa kasuwanci. Ya ce, gwamnati tana yin aiki tukuru wajen inganta ayyukan hidimominta ga al’umma daga dukkan kabilun yankin, tare da taimaka musu wajen zabar ayyuka mafiya dacewa, gami da samun ingantacciyar rayuwa.(Ahmad)