logo

HAUSA

Jakadan Sin a Amurka ya bukaci a karfafa hadin gwiwa a fannin bunkasa aikin gona

2022-04-24 17:40:28 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a kasar Amurka, Qin Gang, ya bukaci kasashen Sin da Amurka su zurfafa hadin gwiwarsu a fannin bunkasa aikin gona mai dorewa, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a yayin rangadin aikinsa a jahohin yammacin tsakiyar Amurka.

Yace, ziyarar aikin da ya gudanar ta ba shi damar ganin gonakin noma masu inganci masu matukar girman gaske, kuma ya kara samun kwarewa game da ayyukan gona na wadannan wurare, Qin ya bayyana hakan ne a babban taron tattauna hadin gwiwar aikin gona na Sin da Amurka na shekarar 2022.

Jakadan yace, Sin da Amurka abokan takarar juna ne, amma kuma abokan taimakon juna ne a harkar kasuwancin amfanin gona, kuma makomar hadin gwiwar kasashen a fannin ayyukan gona ba ta da iyaka. Ya bayyana cewa, akwai bukatar su kara zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin kimiyya, da ilmin fasaha, kana su mayar da hankali wajen samar da cigaba mai dorewa, da tallafawa juna wajen bunkasa fasahohi, da mayar da hankali wajen horar da matasa a fannonin kimiyyar aikin gona da kere-kere.

Qin, ya kuma jaddada bukatar a fadada musayar bayanai da farfado da tsarin tattaunawa a fannin ayyukan gona, ba tare da jinkiri ba.(Ahmad)