logo

HAUSA

Kasar Sin na ci gaba da shan aiki kan ayyukan sararin samaniya

2022-04-24 17:04:18 CMG Hausa

Yau 24 ga watan Afrilu, rana ce ta sararin samaniyar kasar Sin, kuma ranar cika shekaru 52 da samun nasarar harba tauraron dan Adam na farko na kasar mai lamba " DFH-1". A ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 1970, kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam mai suna "DFH-1", yana mai shelar cewa kasar ta shiga zamanin sararin samaniya.

Bayanan da Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a shekarar 2022, hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin za ta ci gaba da "shan aiki". Tashar sararin samaniyar kasar Sin za ta kammala aikin gine-gine a sararin samaniyar, kashi na hudu na aikin binciken duniyar wata da babban aikin gano kananan taurari sun fara aikin bincike a hukumance, ayyukan binciken sararin samaniyar na kasar Sin na kara fadada sabbin fannoni.

Mataimakin daraktan hukumar kula da sararin samaniyar kasar Sin Wu Yanhua, ya bayyana cewa, a bana, an kaddamar da kashi na hudu na aikin binciken duniyar wata a hukumance, kuma kasar Sin ta harba taurarin dan Adam na Chang'e-6, Chang'e-7, da Chang'e-8 a jere, da gudanar da binciken fasahohi masu muhimmanci da kuma gina tashar nazarin kimiyyar duniyar wata ta kasa da kasa.

A cikin 'yan shekarun nan, bisa karuwar nau'o'in tauraron dan Adam da kumbuna daban-daban, tarkacen sararin samaniya da aka samu sakamakon haka ya gabatar da manyan bukatu ta fuskokin tsarawa da gudanar da hanyoyin harba tauraron dan Adam a nan gaba.

Wu Yanhua ya kara bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta kafa wani tsarin lura da kananan taurari dake kusa da doron duniya don tinkarar barazanar cin karon da kananan taurari da ke kusa da doron duniya za su yi, da nufin ba da gudummawa wajen kare duniyarmu da tsaron dan Adam. (Mai fassara: Bilkisu Xin)