logo

HAUSA

An sake samun tashin rikici a masallacin Al-Aqsa dake Jerusalam

2022-04-23 17:04:10 CMG Hausa

Sama da al’ummar Palastinawa 30 aka raunata a tashin hankalin da ya kaure tsakanin jami’an tsaron Israela da Falastinawa a harabar masallacin Al-Aqsa dake birnin Jerusalem a ranar Juma’a. Yan sandan Israela sun  afkawa masallacin bayan da Falastinawa masu bore suka dinga jifarsu da duwatsu da tartsatsin wuta a kusa da katangar masallacin ta bangaren yammaci inda Yahudawa ke bauta, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bada rahoto.

Masallacin, wanda ya kasance wuri mafi tsarki ga mabiya addinin Musulunci, kana wajen bautar Yahudawa, waje ne mai tsarki ga mabiya addinan biyu.

An gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan masu boren na masallacin Al-Aqsa a arewacin zirin Gaza, da Amman, da Jordan, da Dhaka, da kuma Bangladesh.

Rikicin na baya bayan nan ya fara ne a makon jiya bayan jerin munanan hare-haren da Isra’ila ta kaddamar da kuma kama mutane da dama da Isra’ilan tayi a yammacin kogin Jordan.

Bayan lafawar rikicin na ranar Juma’a, sama da Musulmai 150,000 ne suka halarci sallar Juma’a a masallacin.(Ahmad)