logo

HAUSA

An kammala taron dandalin Boao na 2022

2022-04-23 16:49:00 CMG Hausa

Jiya Juma’a 22 ga wata, an kammala taron shekara shekara na dandalin Asiya na Boao mai taken “Annoba da duniya: Ingiza ci gaban duniya da gina makoma tare”, babban sakataren dandalin Li Baodong, ya bayyana yayin taron manema labaran da aka shirya jiya da yammacin ranar cewa, shawarar gudanar da tsaron duniya, babban sakamako ne da aka samu yayin dandalin na wannan karo.

Li Baodong ya kara da cewa, tsaro ya fi muhimmanci yayin da ake kokarin samun ci gaba, kuma ya dace bil adama su hada kansu a yayin da ake kokarin tabbatar da tsaro, don haka shawarar gudanar da tsaro a duniya ta samu amincewa daga bangaren sassa daban daban na mahalartan taron, yanzu haka shawarar ci gaban duniya da shawarar gudanar da tsaro a duniya za su taka babbar rawa kan aikin gina duniya bayan an shawo kan annobar cutar COVID-19.

Hakika an shirya taron dandalin ne karkashin yanayin fama da kalubale iri daban-daban wajen samun ci gaba da tabbatar da tsaro a fadin duniya, Li Baodong ya yi tsokaci cewa, mahalarta taron sun cimma matsaya da dama a fannonin ba da kariya ga lafiyar jikin bil adama, da ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya, da dakile kalubalen tafiyar da harkokin kasa da kasa da dai sauransu. (Jamila)