logo

HAUSA

Adadin litattafan da Sinawan suka karata ya karu a 2021

2022-04-23 16:11:45 CMG Hausa

Cibiyar nazarin dab’in labarai ta kasar Sin ta fitar da sakamakon binciken da aka yi game da karanta litattafai na al’ummun Sinawa karo na 19 a yayin babban taron karanta litattafai karo na farko da aka shirya da yammacin yau Asabar 23 ga wata, inda aka bayyana cewa, adadin litattafan da kowanen Sinawan da suka kai shekarun haihuwa 18 ya karanta a shekara 2021 ya kai guda 4.76, adadin litattafan da ya karanta ta yanar gizo ya kai guda 3.3, duka sun karu bisa na shekarar 2020.

Kana adadin litattafan da kowanen Sinawa wadanda ba su kai shekarun haihuwa 17 ba ya karanta ya kai guda 10.93, adadin da ya karu da 0.22, idan aka kwatanta da shekarar 2020.

Shugaban kasar Xi Jinping ya aike wa babban taron wasikar taya murna, inda ya bayyana cewa, yana fatan daukacin al’ummun Sinawa za su kara nuna kuzari kan karanta litattafai. (Jamila)