logo

HAUSA

Sin ta shirya fuskantar dukkanin kalubale

2022-04-22 21:01:46 CMG Hausa

A ranar Laraba ne ministan ma’aikatar tsaron kasar Sin, da takwaransa na Amurka, suka zanta ta wayar tarho. Wannan ne karon farko bayan watanni 21, da ministocin tsaron sassan biyu suka tattauna. Tsawon lokacin da bangarorin biyu suka kwashe ba tare da sun zanta ba, ya nuna irin kalubale dake tattare da alakar Sin da Amurka.

Ko ma dai mene ne, Amurka ba za ta iya kure kasar Sin ba. Kaza lika, bai dace Amurka ta yiwa Sin kallon hadarin kaji ba, domin kuwa Sin na da jajircewa, da ikon fuskantar duk wani yanayi. (Saminu)