logo

HAUSA

An yanke wa wani Ba-Amurke da ake zargi da aikata kisan kai a Sin hukuncin kisa

2022-04-22 14:07:36 CMG Hausa

               

Matsakaiciyar kotun al’umma a birnin Ningbo dake lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin, ta yankewa Ba-Amurken nan mai suna Shadeed Abdulmateen hukuncin kisa, bayan samunsa da laifin aikita kisan kai da gangan.

A bara ne dai, matar da aka kashe, mai suna Chen, ta rasu tana da shekaru 21 a duniya.

A yayin zaman shari'ar, kotun ta ba da cikakken tabbaci na kare hakkin wanda ake tuhuma, gami da hakkin kariya da samun hidimar tafinta ko fassara, da kuma ziyarar jami’an ofishin jakadancin kasarsa.

Ganin zaman zama da kuma yanke hukunci, kotun ta sanar da babban ofishin jakadanci da kananan ofisohin jakadancin Amurkar dake kasar Sin, kamar yadda doka ta tanada.

Zaman sauraron shari’ar, ya samu halartar mutane sama da 20, da suka hada da ’yan majalisa, da masu ba da shawara kan harkokin siyasa, da sauran jama’a. (Ibrahim)