logo

HAUSA

Kenya za ta fara amfani da sabbin tagwayen hanyoyin mota da Sin ta gina yayin gasar gudun yada kanin wani da za ta gudanar

2022-04-22 14:01:55 CMG Hausa

 

Manyan ’yan wasan kasar Kenya da ma talakawan kasar, za su ci moriyar fara amfani da sabbin tagwayen hanyoyin motar da kasar Sin ta gina a Nairobi, yayin da babban birnin kasar ta gabashin Afrika zai karbi bakuncin gasar gudun yada kanin wani ta Marathon, kamar yadda mashirya gasar suka bayyana a ranar Alhamis.

Gasar ta Nairobi City Marathon, wanda ma’aikatar wasanni da asusun bunkasa jin dadin al’umma na kasar Kenya suka shirya, za ta gudana a ranar 8 ga watan Mayu, gabanin bikin bude titunan motar a hukumance mai tsawon kilomita 27.

A cewar hukumar kula da manyan titunan kasar Kenya, a halin yanzu, masu aikin kwangilar hanyar suna kokarin kammala bangaren karshe na ayyukan titunan, gabanin kaddamar da su, wanda shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai bude.

Ana fatan hanyar za ta rage adadin lokutan da ake shafewa na zirga-zirga tsakanin kudanci zuwa yammacin Nairobi, zuwa mintoci 20 maimakon awoyi biyu da ake shafewa. (Ahmad)