logo

HAUSA

Mutane 34 aka kashe tare da raunata 102 a fashewar abubuwa a arewacin Afghanistan

2022-04-22 14:00:14 CMG Hausa

 

A kalla mutane 34 aka kashe da kuma raunata wasu 102, a sakamakon fashewar tagwayen bama-bamai a arewacin kasar Afghanistan a ranar Alhamis, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bada rahoto.

A garin Mazar-i-Sharif, babban birnin lardin Balkh, an kashe masu ibada a kalla 30 da kuma raunata wasu 80, a lokacin da aka samu fashewar bam na farko a hanyar wani masallaci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Khaama ya jiyo daga wani jami’in asibitin shiyyar Abu Ali Sina ya bayyana.

Bam na biyu ya fashe mintoci 15 bayan na farko a lardin Kunduz mai makwabtaka, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, da raunata wasu 22.

Babu wata kungiya da ta yi ikirarin daukar alhakin kaddamar da harin.

A watannin baya bayan nan, kasar mai fama da yaki, ta sha fuskantar jerin hare-haren ta’addanci daga kungiya mai da’awar kafa daular musulunci ta IS, inda take adawa da gwamnatin rikon kwarya ta Taliban. (Ahmad)