logo

HAUSA

Sin: Tsarin gudanar da tsaro na duniya mataki ne na wanzar da manufar kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya

2022-04-21 19:57:52 CMG Hausa

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping, ke gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, a taron dandalin kasashen Asiya na Boao a Alhamis din nan, ya gabatar da shawarar samar da tsarin tabbatar da tsaron kasa da kasa, wanda zai amfani dukkanin sassa.

Game da hakan, yayin da yake amsa tambaya a taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce shawarar ta shugaba Xi, kari ne kan abubuwan da Sin ke bayarwa gudummawa ga duniya, kuma manufar, mataki ne na wanzar da burin kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya ta fuskar tsaro.

Kaza lika, Wang ya musanta zargin da mataimakin sakataren wajen Amurka ya yi, cewa wai Sin na goyon bayan matakan soji da Rasha ke dauka kan kasar Ukraine, da cewa wai Rasha ta bukaci Sin da ta taimaka mata da kayan aikin soja, yana mai bayyana hakan a matsayin karya da aka kitsa, ba tare da wata shaida ba. (Saminu)