logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin waje: Ana fatan Sweden za ta girmama addinai daban daban

2022-04-21 18:32:27 CMG Hausa

A matsayin martani ga babbar tarzoma da ake fuskantar a Sweden, a jiya Laraba a gun taron ‘yan jarida, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ana fatan bangaren gwamnatin Sweden ya lura da lamarin da ya faru a matsayin wani darasi, ta yadda za ta fara girmama addinai daban daban, ciki har da Musulunci, da kiyaye halastacciyar moriyar masu bin addinan, da aiwatar da alkawarin da ya yi na mutuntawa, da kare ‘yancin biyayya ga addinai.

Bisa labarin da aka bayar, a kwanaki baya, wata jam'iyyar masu tsattsauran ra’ayi a kasar Sweden ta shirya zanga-zangar adawa da Musulunci, tare da kona littattafan Al-Kur’ani a wurare da dama a kasar, lamarin da ya haddasa babbar tarzoma daga bangaren Musulman da ke zama a kasar Sweden, inda aka lalata kayayyakin jama’a, da haddasa jin rauni na wasu mutane da yawa. Ganin abkuwar lamarin ya sa wasu kasashen Musulmai da dama, sun nuna rashin amincewa da takaicinsu ga jakadun kasar Sweden a kasashen. (Safiyah Ma)