Shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi a taron koli na Boao
2022-04-21 11:13:57 CMG HAUSA
An bude taron dandalin tattaunawa tsakanin kasashen nahiyar Asiya na Boao na shekarar 2022 a garin Boao dake lardin Hainan a safiyar yau Alhamis. Kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taro ta kafar bidiyo tare da gabatar da wani muhimmin jawabi.
A jawabinsa, shugaba Xi ya nanata cewa, ya kamata a nace ga neman cika burin da aka sanya a gaba duk da wahalhalu da za a fuskanta.
Ya ce, hanya mafi dacewa wajen tinkarar mawuyacin halin da ake ciki, ita ce hadin gwiwa, saboda daukacin Bil Adama na da makoma ta bai daya. Ya kara da cewa, kasashe daban-daban na da buri iri daya wajen neman samun ci gaba tare, don haka bai kamata a bar wani a baya ba.
Kazalika, ya jaddada cewa, ra’ayin bangaranci da kashin kai da kuma manufar katse hulda da matsin lamba mai tsanani, ba za su samu amincewar duniya ba ko kadan, balle ma a kafa wata kungiya don nuna wariya ga wasu da rura wutar tada rigingimu. Shugaba Xi ya ce, dole ne kasashe masu karfi su zama abin koyi ga saura, su nace ga ka’idar nuna adalci da hadin kai da zama masu sahihanci da martaba shari’a da doka, su kuma sauke nauyin dake wuyansu.
Taron kolin shekara-shekara na Boao na Asiya na bana, zai gudana ne a zahiri da kuma kafar bidiyo daga ran 20 zuwa 22 ga wata, bisa jigon “Annoba da duniyarmu: Bunkasa ci gaban duniyada gina makomar bai daya tare.” (Amina Xu)