logo

HAUSA

Iyalan MDD a Habasha sun yi bikin ranar harshen Sinanci

2022-04-21 11:16:19 CMG HAUSA

 

Jiya ne, iyalan MDD dake kasar Habasha, suka gudanar da bikin ranar harshen Sinanci, da nufin bunkasa harshe da al'adun kasar Sin ta hanyar yayata mabambantan harshe da al'adu.

Bikin tunawa da harshen Sinanci, wanda hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta MDD (UNECA) tare da hadin gwiwar tawagar kasar Sin dake kungiyar tarayyar Afirka (AU) suka dauki nauyin shirya shi, ya gudana ne ta kafar bidiyo, saboda matsalar annobar COVID-19.

Jami'in hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD (UNECA), kuma daraktan sashen kididdiga Oliver Chinganya ya bayyana cewa, bikin ya amince da ranar a matsayin wani muhimmin bangare na kokarin da MDD ke yi na bunkasa bangarori daban-daban, da mabambantan al'adu, da harsuna, da daidaiton amfani da harsuna guda shida da MDD ta amince da su.

Yayin Bikin, an gabatar da jawabai kan harshe da al'adu, da raye-rayen gargajiya na kasar Sin, da gogewar al'adun gargajiya da harshen Sinanci wanda matasan Afirka suka gabatar, da kade-kaden gargajiya na kasar Sin, da wasan Tai Chi, da kuma baje kolin zane-zane na kasar Sin.

A jawabinsa jami'in hulda da jama'a na kasar Sin a kungiyar tarayyar Afirka ta AU, Chen Xufeng ya bayyana cewa, bisa la'akari da karuwar bukatar harshen Sinanci a fadin duniya, tare da karuwar dalibai dake nazarin harshen Sinanci, wasu kasashen Afirka 16 sun riga sun shigar da harshen Sinanci cikin tsarin manhajojin karatunsu.

Iyalan MDD dake kasar Habasha dai, na gudanar da bukukuwan tunawa da ranar harshen Sinanci a kowace shekara, bisa ga shawarar da hukumar raya al'adu da ilimi ta MDD (UNESCO) ta yanke a shekarar 2010, na gudanar da bikin ranar harshen Sinanci a ranar 20 ga watan Afrilun kowa ce shekara. (Ibrahim Yaya)