logo

HAUSA

Matasan kasar Sin na rayuwa a yanayi mafi kyau cikin tarihin kasar

2022-04-21 15:21:09 CMG HAUSA

 

A yau Alhamis, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani mai taken “matasan kasar Sin a sabon zamani”, inda ya bayyana cewa, yayin da suke rayuwa a cikin yanayi mafi kyau a tarihin kasar Sin, matasan wannan zamani na more kyakkyawan yanayin ci gaba da dimbin damarmakin kyautata sana’arsu.

A cewar takardar, sama da matasa miliyan 25 ne suka tserewa talauci yayin da kasar ke samun saurin ci gaba. Tana bayanin cewa, wannan zuri’a na iya sa ran samun kyakkyawar makoma da ci gaba bisa la’akari da yadda damarmakin ci gaba da suke da su, ke da tubali mai kwari.

Ta kara da cewa, bisa la’akari da saurin ci gaban tattalin arziki da zaman takewa, matasa a kasar Sin na cikin wani zamani na tabbatar da daidaito a fannin samun ilimi da dimbin ayyukan yi daban daban da samun ci gaba ba tare da tangarda ba da karin wasu damarmakin ci gaba.

Bugu da kari, takardar ta ce, za su iya kuma samun ci gaba cikin kyautatuwar yanayin doka da more dabarun tallafi masu karfi da hidimomin kulawa da jama’a da kuma karin kula daga hukumomi daban daban. (Fa’iza Mustapha)