logo

HAUSA

Babban jami’in majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ya tattauna da shugabar majalisar dokokin kasar Malawi

2022-04-21 11:17:52 CMG HAUSA

 

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Li Zhanshu ya tattauna da shugabar majalisar dokokin kasar Malawi, Catherine Gotani Hara ta kafar bidiyo a jiya, inda ya yi kira da karfafa muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Li Zhanshu, ya ce Malawi muhimmiyar abokiyar hulda ce ga kasar Sin a Afrika. Kuma a shirye Sin take ta hada hannu da Malawin, wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da ingiza ci gaba.

Ya kara da cewa, kasar Sin na goyon bayan Malawi ta lalubo hanyar ci gaba da ta dace da yanayinta, kuma ta shirya su ci gaba da taimakawa juna kan batutuwan da suka shafi muradunsu.

A nata bangaren, Catherine Hara ta ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Malawi da Sin, dangantakar kasashen biyu da yi ta kyautatuwa. Kuma Malawi na goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Ta kuma yaba da gudunmawa da taimakon da Sin ke ba Malawi ta fuskar raya tattalin arziki da ci gaban harkokin al’umma da kuma yaki da COVID-19.

Har ila yau, ta ce majalisar dokokin Malawi za ta karfafa musaya da majalisar wakilan jama’ar kasar Sin tare da bayar da gudunmawa wajen inganta abota a tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)