logo

HAUSA

Xi ya amsa wasikar da daliban makarantar firamare ta Burtaniya suka aiko masa

2022-04-21 20:05:57 CMG Hausa

Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da daliban makarantar firamare ta Francis Holland ta kasar Burtaniya suka aiko masa, inda ya bayyana ra’ayinsa, game da batun sauyin yanayi.

Xi Jinping ya ce, “Mu iyalai ne dake zaune tare a duniyarmu, kuma sauyin yanayi kalubale ne dake gaban dukkanin bil Adama, don haka ya kamata mu hada kanmu, domin fuskantar wannan kalubale”.

Makarantar Francis Holland, makarantar mata ce dake birnin London, wadda ke sa kaimi ga dalibai, da su mai da hankali kan batutuwan kare muhalli da sauyin yanayi. Cikin ‘yan kwanakin nan, daliban aji na hudu, sun aikawa shugaba Xi Jinping wata wasika cikin hadin gwiwa, inda a cikin ta suka mai da hankali kan batun sauyin yanayi. (Maryam)