logo

HAUSA

Sin: Tsagaita bude wuta da kawo karshen yaki nan da nan ita ce muhimmiyar hanyar warware matsalar jin kai a Ukraine

2022-04-20 10:14:28 CMG HAUSA

 


Jiya ne, agogon wurin, kwamitin sulhu na MDD ya yi bitar batun jin kai a kasar Ukraine.

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya bayyana matukar damuwa game da yanayin jin kai da sauran munanan sakamako da rikicin kasar Ukraine ya haifar. A don haka, bangaren kasar Sin yana son gabatar da shawarwari guda hudu:

Na farko, ya kamata a yi kokarin rage barnar da rikicin ya haifarwa fararen hula. Na biyu, dole ne mu magance matsalar 'yan gudun hijira yadda ya kamata. Na uku, wajibi ne a kara azama wajen inganta shawarwarin diflomasiyya. Na hudu kuma, dole ne mu mai da hankali tare da kawar da mummunan tasirin da takunkumai suka haifar.

A wannan rana, kasashen Amurka, da Burtaniya, da Canada, sun ba da sanarwar cewa, za su aikawa Ukraine karin makaman atilare.

Bugu da kari, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana a wata hirar da ya yi jiya da jaridar Indiya Today da ake wallafawa mako-mako cewa, a yayin da ake fuskantar takunkuman da kasashen yamma suka kakkaba mata, an warware dogaron da Rashan ke yi kan kasashen yamma a fannoni da dama. (Ibrahim)