logo

HAUSA

Kaso na 3 na alluran rigakafin da Sin ta baiwa Zambia ya tashi zuwa kasar

2022-04-20 20:16:28 CMG Hausa

A yau Laraba ne aka aike da kaso na 3, na alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta baiwa kasar Zambia tallafin su. A cewar hukumar kasar Sin mai lura da ayyukan hadin gwiwar ci gaban kasa da kasa, a wannan karo Sin ta aikewa Zambia alluran rigakafi 600,000, a wani mataki na bunkasa kokarin gwamnatin Zambia na samar da kariya ga al’ummun ta.

Ya zuwa yanzu, Sin ta samarwa kasashen Afirka 53 da kungiyar AU, sama da alluran rigakafin cutar COVID-19 sama da miliyan 180.   (Saminu)