logo

HAUSA

An kaddamar da taron Asia na Boao na bana

2022-04-20 20:08:10 CMG Hausa

A yau Laraba ne aka bude taron kwanaki 3, na dandalin tattaunawa na nahiyar Asiya ko Boao na shekarar 2022. Taron mai lakabin "Annoba da duniyar mu: Bunkasa ci gaban duniya da gina makomar bai daya" ya maida hankali ga tattauna batutuwa da dama, da suka hada da kandagarki da shawo kan annoba, da raya tattalin arzikin duniya, da farfadowa ba tare da gurbata muhalli ba, da ci gaba mai dorewa, da raya tattalin arziki da na’urori masu kwakwalwa. Sauran sun hada da hadin gwiwar kasa da kasa da jagorancin duniya, da sabbin hadin gwiwar yankunan Asiya.  (Saminu)