logo

HAUSA

Shirin “Mu fara darasi” zai gayyaci masu sha’awar Sinanci a duniya domin shiga kwas din koyon Sinanci ta Intanet

2022-04-20 14:02:37 CMG HAUSA

 

Yau ne, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG zai gabatar da shiri na musamman mai suna “Mu fara darasi” ta talibijin da kuma manhajarsa, don murnar ranar Sinanci ta MDD, tare kuma da kaddamar da shirin CMG na yayata Sinanci.

An ayyana ranar Gu Yu bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a matsayin ranar Sinanci ta MDD, don tunawa da gudummawar da Cang Jie, wanda ya kirkiro kalmomin Sinanci ya bayar yau shekaru aru-aru da suka gabata. Ranar Gu Yu, shi ne lokacin karshen bazara da tsirrai ke fitowa, a lokacin, adadin ruwan sama na karuwa, sa’an nan tsirrai iri-iri ke fitowa. (Tasallah Yuan)