logo

HAUSA

Ministan tsaron kasar Sin ya zanta da sakataren tsaron Amurka

2022-04-20 21:12:13 CMG Hausa


 

A yau Laraba ne dan majalissar gudanarwa, kuma ministan tsaron kasar Sin Wei Fenghe, ya zanta ta wayar tarho da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin.

Yayin tattaunawar ta su, jami’an biyu sun yi musayar yawu game da tsaron teku, da na sararin samaniya, da kuma yanayin da ake ciki a Ukraine. Kaza lika bangaren Sin ya bukaci Amurka, da ta dakatar da aiwatar da matakan da ka iya tada tarzoma a sassan teku. Kana ta kauracewa amfani da yanayin da ake ciki a Ukraine, wajen bata suna, ko shafawa Sin bakin fenti, ko kuma yiwa Sin din barazana.   (Saminu)