logo

HAUSA

Sin da Ghana sun yi alkawarin karfafa hadin gwiwa

2022-04-20 10:19:01 CMG HAUSA

 

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a ranar Talata ya tattauna da ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey ta wayar tarho, inda bangarorin biyu suka bukaci a kara gina hulda ta kut-da-kut a tsakaninsu.

Wang ya taya Ghana murnar nada ta mambar wucin gadi a kwamitin sulhun MDD daga shekarar 2022 zuwa 2023, kuma yana fatan kasar za ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Wang ya ce, kasar Sin ta kafa dandalin kawancen abokai na shawarar bunkasa ci gaban duniya karkashin tsarin MDD, domin tallafawa farfado da tattalin arziki na kasashe masu tasowa bayan kawo karshen annobar COVID-19. Ya kara da cewa, ana maraba da Ghana ta shigo kawancen, domin samun cikakken karfin aiwatar da ajandar samar da dawwamamman ci gaba nan da shekarar 2030.

Ya ce, a ko da yaushe kuri’ar da kasar Sin ke jefawa a MDD, tana goyon bayan kasashe masu tasowa ne, da ’yan uwanta na Afrika. Wang ya bukaci a kara zurfafa hadin gwiwa wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa bisa daidaito, da adalci, kuma a nuna adawa ga manufar nuna danniya da amfani da karfin ikon siyasa, kuma a tabbatar da kiyaye dukkan moriyar kasashen biyu da sauran kasashe masu tasowa.

A nata bangaren, Botchwey ta ce, kasar Ghana tana matukar farin ciki da manyan nasarorin ci gaba da kasar Sin ta samu, da ingantaccen jagoranci na shugaba Xi Jinping. Ta kara da cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu ya samar da muhimmin kwarin gwiwa ga kasashen Afrika. (Ahmad Fagam)