logo

HAUSA

Mummunan hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Nijeriya

2022-04-20 15:38:41 CMG HAUSA

 

Jiya ne, wata motar bas ta yi taho mu gama da wata mota a jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Nijeriya, inda mutane 20 suka gamu da ajalinsu kana mutum guda ya jikkata.

Yusuf Abdullahi, shugaban hukumar kiyaye hadurra a kan tituna ta kasa reshen jihar Bauchi, ya shaidawa taron manema labarai a garin Bauchi, fadar mulkin jihar cewa, wata bas da wata mota sun yi karo da juna a kusa da kauyen Huturu, kuma binciken farko ya nuna cewa, hadarin ya faru ne sakamakon tukin ganganci da gudun da ya wuce kima. (Safiya Ma)