logo

HAUSA

Masana'antu a Shanghai sun dawo aikin samar da kayayyaki

2022-04-20 16:25:58 CMG Hausa

Kamfanonin samar da kayayyaki dake birnin Shanghai na gabashin kasar Sin, sun dawo aikin samar da kayayyaki, duk da tsauraran matakan yaki da COVID-19 da aka sanya a birnin.

A baya-bayan nan dai, kasar Sin ta kaddamar da rukunin farko na kamfanoni 666 dake Shanghai, wadanda suka cancanci sake dawowa aikin samar da kayayyaki, kuma da yawa daga cikinsu suna cikin bangaren samar da kayayyaki, kamar kamfanonin kera motoci, da masu kera muhimman sassan kwanfuta, da kamfanonin harhada magunguna. (Ibrahim)